Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Amurka tana yunkurin hana bunkasuwar kasar Sin ta hanyar batun hakkin bil Adama
2019-12-08 16:52:30        cri
A kwanakin baya, asusun kula da hakkin bil Adama na kasar Sin ya gudanar da taron tattaunawa kan dokar hakkin bil Adama na Uygur na yankin Xinjiang da kasar Amurka ta zartas, inda masanan hakkin bil Adama na kasar Sin sun yi amfani da hakikanin batutuwa don shaida cewa kasar Amurka ta kyale bunkasuwar yankin Xinjiang da nasarorin da ya samu, ta yi bayani game da yankin ba tare da tushe ba, tana yunkurin hana bunkasuwar kasar Sin ta hanyar batun hakkin bil Adama.

Direktan zartaswa na cibiyar nazarin hakkin bil Adama ta jami'ar Renmin ta kasar Sin Zhu Liyu ya bayyana cewa, tun da aka kafa sabuwar kasar Sin, an samu babban ci gaba a yankin Xinjiang. Bisa kididdigar da aka yi, tun daga shekarar 1952 zuwa 2018, yawan GDP na yankin Xinjiang ya karu da ninki 200, yawan GDP na kowane mutum dake yankin ya karu daga Yuan 160 zuwa Yuan dubu 49, wanda ya shaida cewa, Amurka ta zartas da wannan doka ba tare da tushe ba, ta yi bayani game da yankin Xinjiang ta hanyar nuna shakka da yin tunani.

Mataimakin shugaban kungiyar nazarin hakkin bil Adama ta kasar Sin Shen Yongxiang ya yi nuni da cewa, kasashe da dama sun nuna amincewa ga manufofin kawar da tsattauran ra'ayi na kasar Sin. Kasar Amurka ta hada wasu kasashe yammacin duniya don bayar da sanarwa game da batun yankin Xinjiang na kasar Sin, kana majalisar wakilai ta kasar Amurka ta zartas da doka, wannan aikin tsoma baki kan harkokin cikin gida na kasar Sin, shi ne ra'ayin bangare daya. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China