Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Muna kin duk wanda ke son bata hadin gwiwar al'ummomin jihar Xinjiang, in ji mutanen bangarori daban daban na jihar
2019-12-10 14:25:40        cri

Kwanan baya, mutanen jihar Xinjiang na kabilu daban daban, da na bangarori daban daban sun bayyana cewa, dokar hakkin dan Adam da Amurka ta fidda kan jihar Xinjiang karya ce kawai, kuma ba za su yarda da duk wanda ke son bata yanayin zaman karko da hadin gwiwar al'ummomin jihar Xinjiang ba, kuma tabbas ne, jihar Xinjiang za ta sami makoma mai haske.

Shugabar kwamitin kula da harkokin dokoki na zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar jihar Xinjiang Li Juan ta bayyana cewa, "dokar hakkin dan Adama kan kabilar Uygur ta shekarar 2019" da kasar Amurka ta fidda, ta zama harkar tsoma baki mai tsanani cikin harkokin gidan kasar Sin. Ta ce, "Wace yarjejeniyar kasa da kasa ta baiwa kasar Amurka wannan iko? Har ta tsoma baki cikin harkokin gida na kasashen ketare, ta kuma yi zargi maras tushe! Ya kamata a zartas da wani daftari bisa doka, tambayata ita ce, wace doka kasar Amurka take bi don ta yi bincike kan harkokin gida na kasashen waje? Lalle wannan dokar ta ba ni dariya."

Mataimakin shugaban hukumar albarkatun ruwa ta jihar Xinjiang Ilihan Osman ya bayyana cewa, dokar hakkin dan Adam kan jihar Xinjiang da kasar Amurka ta fidda doka ta karya, ba ta fadi gaskiya ba. Yana mai cewa, "A matsayin wani jami'i na kabilar Uygur a jihar Xinjiang, ban yarda da wannan doka ba, kuma dokar ta bata raina kware da gaske! A halin yanzu, muna cikin zaman karko a jihar Xinjiang, kuma cikin shekaru 3 da suka gabata, ba mu taba gamuwa da harin ta'addanci ba. Al'ummomin kabilu daban daban suna zaman lumana, suna da imanin kiyaye zama lafiyar zaman takewar al'umma a jihar. Muna goyon bayan Jam'iyyar Kwaminis ta Kasar Sin kan gudanarwar harkokin jihar Xinjiang, kuma muna yarda da dukkanin sanarwar da gwamnatin kasar Sin ta fidda kan kasar Amurka."

A nashi bangare, mataimakin shugaban hukumar kimiyya da fasaha ta jihar Xinjiang Gao Wangsheng ya ce, a matsayin wani jami'in da gwamnatin tsakiya ta tura wa jihar Xinjiang, ya gane ma idonsa canje-canje da ci gaba da jihar Xijiang ta samu cikin shekaru da dama da suka gabata. Yanzu, tattalin arzikin jihar yana ci gaba da karuwa, al'ummomin jihar suna cikin zaman lumana, tare da samun kyautatuwar zaman rayuwarsu, mutane na kabilu daban daban suna fahimtar juna, lalle al'ummomin kabilu daban daban a jihar suna hada kansu kwarai da gaske. Ya ce, "Ina nan jihar Xinjiang sama da shekaru biyar, cikin 'yan shekarun nan, jihar Xinjiang tana bunkasuwa cikin sauri. Wasu kamfanonin kirkire-kirkire sun shiga jihar, harkokin masana'antu na bunkasuwa cikin sauri, ana kuma samun karin kwararru a nan jihar, lamarin da ya nuna cewa, yanayin zaman karko na jihar Xinjiang yana ci gaba da samun kyautatuwa."

Wani dalibin da ya riga ya gama karatunsa a cibiyar ilmantarwa da horaswa ta birnin Hotan na jihar Xinjiang Kasimcan Helil ya nuna kin yarda kan dokar hakkin dan Adam da majalisar wakilan kasar Amurka ta fidda. Ya ce, "A makarantarmu, na koyi ilmi da fasahohi da dama, yanzu, na kawar da tsattsauran ra'ayina game da kabila, har ma na samu karin ilmi sosai game da dokoki. Bayan na kammala karatuna a makarantar, na kafa kamfani na kaina, idan ban taba karatu a makarantar ba, ba zan iya cimma wannan nasara ba! Muna goyon bayan manufofin gwamnati kan jihar Xinjiang, muna kuma goyon baya dukkanin sanarwar da gwamnatin kasar Sin ta fidda kan kasar Amurka!"

Mambar majalisar ba da shawarwari kan harkokin siyasa ta kasar Sin dake jihar Xinjiang, kana mataimakiyar shugabar kungiyar 'yan wasan fasahar raye-raye ta kasar Sin Dilnar Abdullah tana mai cewa, "A halin yanzu, muna cikin zaman karko da samun jituwa a tsakanin kabilu daban daban a jihar Xinjiang, al'ummomin jihar suna hada kansu, suna kuma jin dadin zamansu a nan. Ina son gaya wa dukkanin mambobin majalisar wakilan kasar Amurka cewa, ku daina tsoma baki cikin harkokin gidan kasarmu, kuma ba ku da ikon suka kan harkokin hakkin dan Adam na kasarmu. " (Maryam Yang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China