Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Amurka tana yunkurin tsoma baki kan harkokin cikin gida na kasar Sin ta hanyar batun hakkin bil Adama na yankin Xinjiang
2019-12-08 16:51:41        cri

A kwanakin baya, majalisar wakilai ta kasar Amurka ta zartas da dokar hakkin bil Adama na Uygur ta shekarar 2019, inda ta zargi yanayin hakkin bil Adama na yankin Xinjiang na kasar Sin ba tare da tushe ba, da kin amincewa da kokarin Sin na yaki da ta'addanci da kawar da tsattsauran ra'ayi, da kuma tsoma baki kan harkokin cikin gida na kasar Sin. Game da wannan batu, direktan zartaswa na jaridar Al-Ahram ta kasar Masar Mansour Abo Alazzm ya bayyana cewa, yankin Xinjiang yana cikin yanayin samun zaman lafiya da bunkasuwa, Amurka tana yunkurin tsoma baki kan harkokin cikin gida na kasar Sin ta hanyar batun hakkin bil Adama na yankin Xinjiang.

A yayin da yake ziyara a kasar Sin, Mansour ya taba ziyartar yankin Xinjiang sau biyu, game da yanayin yankin, ya bayyana cewa, ana samun zaman lafiya da wadata a yankin Xinjiang a halin yanzu domin gwamnatin yankin da jama'ar yankin sun yi kokari tare don samun bunkasuwa tare.

Mansour ya nuna yabo ga cibiyar horar da fasahohin sana'a da aka kafa a yankin Xinjiang. A ganinsa, ya kamata a tabbatar da hakkin bil Adama na jama'ar yankin don kawar da mugun tasirin da ta'addanci da tsattsauran ra'ayi suka kawo musu, ta hakan za a samu zaman lafiya mai dorewa a yankin. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China