![]() |
|
2019-12-06 09:39:31 cri |
Mambobin kwamitin, da masu ba da shawara kan harkokin siyasa daga kungiyoyin kananan kabilu da wakilan manyan kungiyoyin addinai biyar dake kasar Sin, sun yi karin haske yayin taron karawa juna sani da kwamitin ya shirya, inda suka yi fatali da karairayi da maganganun marasa tushe dake cikin dokar, sannan suka yi bayani daki-daki kan halin da ake ciki a yankin.
Mahalarta taron sun bayyana cewa, bangaren Amurka dai, yana kokarin illata matakan kasar Sin na yaki da ta'addanci da tsattsauran ra'ayi, da goyon baya da ma karfafa gwiwar shiga harkokin da bai shafe ta ba, yin zagon kasa, ayyukan ta'addanci da raba kan kabilu da tsattsauran ra'ayin addini.
Sun bayyana cewa, irin wannan mataki na 'yan siyasar Amurka, tamkar tsoma baki ne a harkokin cikin gidan kasar Sin da ma nuna ra'ayinsu na nuna dannayi, kuma kasar Sin ba za ta lamunta ba ko kadan. (Ibrahim Yaya)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China