Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kwamiti mai kula da harkokin waje na NPC da dai sauran hukumomi sun ba da sanarwa kan dokar hakkin Bil Adama na Uygur da Amurka ta gabatar
2019-12-04 14:36:26        cri
Kwamitin kula da harkokin waje na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin NPC, da kwamitin kula da harkokin waje na majalisar ba da shawara kan siyasa ta kasar Sin CPPCC, da ofishin yaki da ta'addanci na kasar Sin, da kuma kwamitin kula da harkokin kabilun kasar Sin, da zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar jihar Xinjiang mai cin gashin kanta sun ba da sanarwa kan dokar hakkin Bil Adama ta Uygur da Amurka ta gabatar a yau Laraba, inda suka nuna matukar rashin jin dadi da ma adawa da zargin da Amurka take yiwa kasar ba gaira ba dalili kan ayyukan yaki da ta'addanci da Sin take gudanarwa a jihar Xinjiang, matakin da ya kasance tsoma baki a harkokin cikin gidan kasar Sin.

Rahotanni na cewa, manufar kafa da kuma gudanar da cibiyar koyar da sana'o'i a Xinjiang ita ce kawar da tushen yaduwar ta'addanci da tsattsauran ra'ayin addini, matakin da ya cimma nasarar hana aukuwar ayyukan ta'addanci da kare rayuwa da dukiyoyin jama'ar kabilu daban-daban a wurin.

Kasar Sin tana kalubalantar Amurka da ta yi watsi da bambancin ra'ayi a siyasance kan kasar Sin, da kuma jingine matakan da ta dauka na matsawa kasar Sin lamba, kana ta dakatar da zargin kasar Sin ba bisa gaskiya ba, da daina tsoma baki a harkokin cikin gidan kasar Sin, da dakatar da yin abubuwan da za su bata hadin kan kasashen biyu kan aikin yaki da ta'addanci. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China