Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xinjiang ta ba da wata sanarwa kan dokar hakkin Bil Adama na Uygur ta shekarar 2019 da Amurka ta zartas
2019-12-04 14:21:44        cri

Yau Laraba, kwamitin gudanarwa na harkokin jihar Xinjiang mai cin gashin kanta, karkashin majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama'ar kasar Sin, ya ba da wata sanarwa a hukumance, kan dokar hakkin Bil Adama na Uygur ta jihar Xinjiang na shekarar 2019 da Amurka ta zartas.

Sanarwar ta ce, ta'addanci makiyin duk Bil Adama ne, wajibi ne duk al'ummar duniya su hada kai wajen dakile shi. Xinjiang muhimmin fage ne na tinkarar ta'addanci a duniya, tun shekaru 90 na karni na 20 zuwa shekarar 2016, 'yan aware na gida da waje, da masu tsattsauran ra'ayin addini, da masu tarzoma, sun kai dubban hare-hare jihar, lamarin da ya haddasa mutuwar fararen hula da dama, yayin da 'yan sanda fiye da dari suka rasa rayukansu, matakin da ya kawo babbar illa ga rayuwa da dukiyoyin jama'a, har ya keta hakkin Bil Adama da kawo cikas ga bunkasuwar tattalin arziki da al'ummar jihar Xinjiang. Hakan ya sa, gwamnatin jihar ta dauki matakan da suka dace don dakile 'yan aware da tsattsauran ra'ayin addini da yaki da karfin tuwo, matakin da ya hana aukuwar ayyukan ta'addanci da kaiwa ga samun ci gaba mai armashi a mataki-mataki a wadannan fannoni, da kuma tabbatar da hakkin jama'ar jihar a fannoni daban-daban. Har ila yau, Xinjiang ba ta gamu da ta'addanci ba cikin shekaru 3 a jere, har yawan laifufukan da aka tafka ya ragu sosai.

" Gani ya kori ji, duniya na ganewa idonta ci gaban da Xinjiang ke samu a fannin yaki da ta'addanci, kuma munafuncin dodo ya kan ci mai shi, Amurka ta dauki fuska biyu a wannan fanni, kuma za ta girbi abun da ta shuka " , kamar yadda aka rubuta a cikin wannan sanarwa. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China