Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Rahoton Da The New York Times Ta Wallafa Game Da Xinjiang Ba Gaskiya Ba Ne
2019-11-19 14:34:51        cri

Mai Magana da yawun gwamnatin al'ummar jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kanta, ya bayyana cewa, jiha ce da kasar Sin ke kokarin kawar da ayyukan ta'addaci da tsattsauran ra'ayi. Bayanai na nuna cewa, daga shekarar 1990 zuwa karshe 2016, an aikata dubban ayyukan dake da nasaba da ta'addanci a jihar ta Xinjiang, lamarin da ya shafi dubban mutane da ba su san hawa ba balle sauka, baya da kadarori da aka yi hasara.

A saboda irin wannan mummunan yanayi da ake ciki, Xinjiang ba kawai bisa dokokin kasar Sin, har ma da yadda al'ummomin kasa da kasa ke gudanarwa, matakin da kasar Sin ta ke dauka, ya samu goyon bayan jama'a daga dukkan kungiyoyin kalibu dake jihar. Har ma ba a samu tashin hankali mai nasaba da ta'addanci ba kusan watanni 35 a jere.

Kana tun karshen shekarar 2018, sama da kungiyoyin jami'ai, da kafofin watsa labarai da kungiyoyin addinai, da masana da kwararru daga kasashe da yankuna fiye da 70 ne suka ziyarci jihar ta Xinjiang, inda suka yaba da matakan yaki da ayyukan ta'addancin da ake dauka a jihar, wanda ya dace a koya.

Ya ce, bayanai da jaridar ta ce ta samu, wadanda ke bayyana yadda kasar ta shirya tsare musulmai, sam shirme ne. A baya ma dai, the New York Times ta shiga rudanin da ya kai ga zubar mata da kima sakamakon zamba. A wannan karo, ta wallafa labarin karya game da Xinjiang. Irin wannan hali na nuna tsana, zai sa jama'a masu hangen nesa a duniya su raina ta. (Ibrahim Yaya )

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China