![]() |
|
2019-12-04 11:08:16 cri |
Jihar Xinjiang ta kasar Sin na fama da masu tsattsauran ra'ayi da ayyukan ta'addanci. Saboda ganin irin hali mai tsanani da take ciki, gwamnatin jihar ta dauki matakan da suka dace don dakile su, a sa'i daya kuma, tana mai da hankali kan kawar da asalin wadannan mummunan ayyuka, ciki hadda sa kaimi ga aikin kawar da tsattsauran ra'ayi, matakin da ya ba da tabbacin cewa, ba a samu ayyukan ta'addanci a jihar ba har tsawon shekaru 3 a jere, hakan ya sa mutanen jihar miliyan 25 ke farin ciki sosai da maraba da wadannan manufofi, matakin da ya taka rawa ga aikin yaki da ta'addanci a duniya.
Ban da wannan kuma, kasashen duniya na yabawa wadannan manufofi sosai. Saboda haka, matakin da Amurka ta dauka ya sabawa hakikanin halin da ake ciki da ra'ayin al'ummar duniya, Hua ta yi gargadin cewa, harkokin jihar Xinjiang harkokin cikin gidan kasar Sin ne, ba wanda zai iya tsoma baki a ciki. Kuma ta yi kira ga Amurka da ta daina yin kuskure, tare da dakatar da zartas da wannan doka da tsoma baki cikin harkokin cikin gidan kasar Sin, tana mai cewa, Sin za ta mayar da martani ga duk matakin da Amurka za ta dauka. (Amina Xu)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China