Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Amurka ta sake tsoma baki kan harkokin jihar Xinjiang ta kasar Sin
2019-09-03 20:24:25        cri

A 'yan kwanakin baya, ministan harkokin waje na kasar Amurka Mike Pompeo, ya fidda wani bayani ta yanar gizo, inda ya yi magana maras tushe kan cibiyar ba da ilmin fasahar sana'o'i da Sin ta kafa a jihar Xinjiang.

Game da wannan batu, mai magana da yawun ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin Geng Shuang, ya bayyana a yau Talata a birnin Beijing cewa, babu sauran abin da Amurka ke mai da hankali a kai, illa zargin kasar Sin ba gaira ba dalili, kuma Sin ta nuna matukar rashin jin dadin ta, kana ko alama ba za ta yarda da hakan ba.

A gun taron manema labarai da aka saba yi a wannan rana, Geng Shuang ya ce, harkokin jihar Xinjiang harkokin cikin gidan kasar Sin ne, ba kuma wanda ke da ikon tsoma baki a cikin su.

A kwanan baya gwamnatin kasar Sin, ta gabatar da takardar bayyana ra'ayinta, wadda ke cewa dalilin kafa wannan cibiya shi ne kubutar da wadanda ra'ayin ta'addanci ya ritsa da su, ko mutane da suka aikata laifuka, don su bar wadannan dabi'u nasu.

Ya zuwa yanzu, Xinjiang na cikin yanayi na zama lami lafiya, da samun bunkasuwar tattalin arziki yadda ya kamata, kuma an samu fahimtar juna tsakanin mabambanta kabilu dake jihar.

Geng Shuang ya kara da cewa, kwanan baya, jakadu, ko wakilin jakadun kasashen Nijeriya, da Laos, Cambodia, Philipines, Nepal, Sri Lanka, Bahrai, sun kai ziyara jihar ta Xinjiang, don ganin yadda ake gudanar da ayyuka a cibiyar. Kuma dukkansu sun jinjinawa ayyukan da gwamnatin kasar Sin ke yi, game da dakilewa, da kuma kandagarkin ta'addanci a jihar. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China