Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jakadun kasashen waje sun jinjinawa ci gaban kare hakkin Bil Adama da Sin take samu a jihar Xinjiang
2019-09-19 14:22:07        cri

Jiya Laraba a ofishin MDD dake Geneva, tawagar dindindin ta kasar Sin dake Geneva ta kira taron karawa juna sani kan ci gaban da Sin take samu ta fuskar kare hakkin Bil Adama a jihar Xinjiang, inda wasu jakadun kasa da kasa da suka ziyarci jihar a kwanan baya da wasu masanan kare hakkin Bil Adama na kasar Sin suka yi bayyani a wannan fanni.

Wakilin dindindin na kasar Sin dake Geneva Chen Xu ya yi jawabi cewa, cibiyar horas da sana'o'i da aka kafa a jihar Xinjiang da sauran matakan da jihar ta dauka sun taimaka wajen hana yaduwar ayyukan ta'addanci da tsattsauran ra'ayi. Bayanai na nuna cewa, babu wani tashin hankali da ya barke a cikin shekaru 3 da suka gabata a jihar, jama'ar Xinjiang na kabilu daban daban suna jin dadin zaman rayuwarsu mai cike da tsaro. Ci gaban da jihar Xinjiang ya samu ya zama kyakkyawan abin koyi ga kasashen duniya a fannin yaki da ta'addanci da kawar da tsattsauran ra'ayi. Sin na fatan kara cudanya da sauran kasashe kan lamarin.

Wakilan kasashen Yemen, Zambiya dake Geneva da mataimakin wakilin dindindin na Zimbabwe dake Geneva su ce, sun yi hira da daliban dake samun horo a cibiyar kuma sun ga yadda suke jin dadin rayuwarsu. Sin ta samu ci gaba mai kyau wajen yaki da ta'addanci da kawar da tsattsauran ra'ayi, matakin da ya zama abin koyi ga sauran kasashe a wannan fanni. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China