Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gwamnatin Xinjiang ta yi tir da matakin wasu kafofin watsa labarai na waje bisa yayata bayanan karya
2019-11-29 10:47:47        cri

Kakakin gwamnatin yankin Xinjiang na Uygur mai cin gashin kansa na kasar Sin, ya yi tir da yadda wasu 'yan jaridun yammacin duniya suka dage wajen yayata batun takardun karya da ake yadawa, game da matakan yankin na yaki da ta'addanci da tsattsauran ra'ayi.

Kakakin gwamnatin yankin ya ce wasu kafafen watsa labarai na yammacin duniya, sun yi tsayin daka wajen kare bayanan dake kunshe cikin wadancan takardu, wadanda wasu bata gari suka ce sun samo su ta wasu kafofin sirri, lamarin da a cewar jami'in, kasar Sin ba za ta taba amincewa da hakan ba.

Cikin wata sanarwa da kakakin yankin ya fitar ta shafin intanat na Tianshan na gwamnatin yankin, ya ce abun takaici ne ganin yadda wasu kafofin watsa labarai ke yada wadannan karairayi, da nufin shafawa manufofin tabbatar da tsaron yankin kashin kaji.

Ya ce irin wannan mataki na watsi da gaskiya, da kokarin dakile aniyar al'ummun yankin na Xinjiang na samun kyakkyawan yanayin zamantakewa, da daidaito, abu ne da ba za a taba amincewa da shi ba.

Bugu da kari jami'in ya ce, samar da cibiyar koyar da sana'o'i da ba da horo bisa doka a yankin na Xinjiang, ba ya nufin kafa wani sansani na tsare jama'a. Kuma wadanda ke samun horo a cibiyar ba sa fuskantar wata tsangwama ko gallazawa, yayin da kuma ake tabbatar da kare 'yancin daukacin daliban dake cibiyar bisa tanajin doka. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China