Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xinjiang ta inganta shirin kiwon lafiya don rage talauci da ake gamuwa da shi sakamakon cutuka
2019-08-27 10:19:01        cri
Jihar Xinjiang Uygur mai cin gashin kai dake shiyyar arewa maso yammacin kasar Sin, ta cimma nasarar rage adadin iyalan dake fama da talauci lamarin da ya hana su sukunin biyan kudaden magani, godiya ga shirin kula da lafiya na gwamnatin yankin, kamar yadda hukumar lafiyar yankin ta bayyana a ranar Litinin.

Akwai iyalai 40,000 dake fama da talauci har ba su iya biyan kudaden magani a jahar Xinjiang daga farkon watan Ogusta, adadin ya ragu zuwa kasa da 22,000 a shekarar da ta gabata, Mutalifu Rouzi, daraktan hukumar lafiyar na yankin Xinjiang Uygur mai cin gashin kai ya tabbatar da hakan.

Mutalifu Rouzi ya ce, shirin tallafin gwamnatin ya dauki nauyin biyan magungunan cutuka masu tsanani wadanda aka kara adadinsu zuwa 32.

Talauci da mazauna yankuna hudu na kudancin jahar Xinjiang da suka hada da Hotan, Kashgar, Aksu da Kizilsu Kirgiz, su kan gamu da shi a sanadiyyar yaduwar cutar tarin TB a yankunan. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China