Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jakadun kasashen waje 7 sun ziyarci jihar Xinjiang
2019-08-24 15:38:28        cri
Wasu jakadu da jami'an diflomasiyya daga wasu kasashen duniya 7 sun kai ziyara jahar Xinjiang mai cin gashin kanta ta Uygur daga ranar 19 zuwa 21 ga watan Ogasta bisa goron gayyatar da jami'an gwamnatin shiyyar suka basu.

Jami'an diflomasiyyar daga kasashen Laos, Cambodia, Philippines, Nepal, Sri Lanka, Bahrain da Najeriya sun ziyarci biranen Urumqi da Turpan, domin fahimtar yanayin karfin tattalin arziki da cigaban yankin.

Jami'an sun auna irin kokarin da gwamnatin kasar Sin ke yi wajen bunkasa tattalin arzikin kananan yankuna, da inganta yanayin zaman rayuwar al'umma, da bada 'yancin yin addini, da kuma yaki da ayyukan ta'addanci bisa tsarin doka, sun bayyana cewa nasarorin da jahar Xinjiang ta samu abin koyi ne.

A babbar cibiyar taron baje koli na kasa da kasa ta Xinjiang, jami'an diflomasiyyar sun kalli wani shiri dake bayyana muhimman al'amurran da suka shafi ta'addanci a yankin.

Baba Ahmad Jidda, jakadan Najeriya a kasar Sin, yace Najeriya ta sha fama da matsalar ayyukan ta'addanci a shekaru da dama, kuma har yanzu ana yawan samun matsalolin hare haren a sassan kasar.

Yace ta'addanci da tsattsauran ra'ayi suna daga cikin manyan abokan gaba game da wayewar kan bil adama. Tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali shine babban burin dukkannin kasashen duniya. Ya kamata a hada hannu don yin aiki tare wajen kawar da barazanar ayyukan ta'addanci.

Ya kara da cewa, daukar matakan rigakafin ayyukan ta'addanci ya haifar da kyakkyawan sakamako a jahar Xinjiang saboda an shafe kusan shekaru 3 ba'a samu rahoton hare haren ta'addanci ba. Yace wannan wani muhimmin sako ne ga sauran kasashe. Kana yana fatan kasashen biyu zasu karfafa yin musaya da hadin gwiwa da tallafawa juna wajen yaki da ta'addanci a nan gaba.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China