Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kwararrun Kasa Da Kasa Sun Nuna Cewa, Amurka Tana Tsoma Baki Cikin Harkokin Gidan Sin
2019-12-02 15:04:58        cri
Kwanan baya, kasar Amurka ta zartas da dokar hakkin dan Adam da tsarin dimokuradiya na yankin Hong Kong na kasar Sin, dangane da wannan batu, kwararrun wasu kasashen duniya sun nuna cewa, kasar Amurka tana tsoma baki cikin harkokin gidan kasar Sin, bisa hujarta ta kare hakkin dan Adam da tsarin dimokuradiya, domin hana bunkasuwar kasar Sin. Lamarin da ya bata ran al'ummomin kasa da kasa da kuma nuna halin Amurka na son kai.

Marubucin kasar Faransa Maxime Vivas ya ce, ko shakka babu, kasar Amurka tana tsoma baki cikin harkokin gidan kasar Sin. Shi ya sa, ya kamata a sake jaddada cewa, yankin Hong Kong wani bangare ne na kasar Sin.

Tsohon shugaban ofishin harkokin kasa da kasa na jihar Hessen ta kasar Jamus Michael Borchmann ya ce, bai dace kasar Amurka ta zartas da wannan dokar dake shafar yankin Hong Kong na kasar Sin ba. Kasar Amurka tana son tsoma baki cikin harkokin gidan kasashen waje. Kasar Jamus da kasar Rasha ba su da nisa, kuma suna ciniki da juna. A duk lokacin da suke son kulla yarjejeniya, kasar Amurka za ta yi gargadi kan kasar Jamus, lamarin da ya kuma haddasa illa ga kasashen Turai baki daya.

Shehun malamin cibiyar nazarin harkokin Sin ta kasar Italiya, kana shehun malami a sashen siyasa na jami'ar Luiss ta birnin Rome, Silvia Menegazzi ya bayyana cewa, babban ka'idar da ake bi shi ne, warware harkokin kasa da kasa ba tare da tsoma baki cikin harkokin gidan kasashen waje ba. A halin yanzu, ya kamata a dakatar da tashe-tashen hakula a yankin Hong Kong. Ya ce yankin Hong Kong ya gamu da matsalar zirga-zirga da ta gudanarwar harkokin yankin, kasar Sin ba za ta so haka ba, kuma ko su ma a nahiyar Turai kuma, ba su son haka. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China