Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta jaddada kin amincewa da zartas da kudurin dokar Amurka da ya shafi yankin Hong Kong
2019-11-28 10:46:00        cri

Ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, ta ce gwamnati da al'ummar kasar Sin, ba za su taba amincewa da zartas da kudurin dokar nan ta majalissar dattawan Amurka, wadda ta shafi 'yancin bil Adama da dimokaradiyya a yankin Hong Kong ba.

Wata sanarwa da ma'aikatar ta fitar ta nuna cewa, tsoma baki cikin harkokin yankin Hong Kong, da harkokin cikin gidan Sin, sun sabawa dokokin kasa da kasa, da ma ka'idojin cudanyar kasashe daban daban. Kaza lika hakan wani salo ne na danniya. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China