Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Munafuncin dodo ya kan ci mai shi
2019-12-01 16:45:41        cri
Babban gidan rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG ya bada sharhi a yau Lahadi mai taken "Babu tantama nuna rashin adalci zai sha kaye".

Sharhin ya ce, tada rigingimu mummunan laifi ne da aka aikata wanda babu wata kasa da za ta amince da shi ba. Idan wani rikici ko tashe-tashen hankali kamar irin na Hong Kong suka wakana a kasar Amurka, hukumomin tsaron kasar za su dauki tsauraran matakai don kwantar da tarzoma. Amma ga tashe-tashen hankalin da suka barke a yankin Hong Kong na kasar Sin, Amurka ta yi ikirarin cewa wai matakai ne da wasu mutanen Hong Kong suka dauka domin neman bin tafarkin demokuradiyya. Hakan ya shaida irin rashin adalci ko gaskiya da wasu 'yan siyasar Amurka suka nuna domin nuna danniya ko babakere.

Yayin da mazauna yankin Hong Kong ke alla-allar ganin dawowar zaman doka da oda gami da kwanciyar hankali a wurinsu, Amurka ta zartas da shirin doka da ta shafi Hong Kong, don hura wutar rikici, al'amarin da ya shaida irin rashin adalcin da ta nuna. Ya kamata Amurka ta gane cewa, munafuncin dodo ya kan ci mai shi.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China