2019-12-02 11:02:41 cri |
Shugaban kungiyar 'yan kasuwar shige da fice na yankin Hong Kong na kasar Sin Lam Lung-on yana ganin cewa, kasar Amurka ta zartas da dokar ce domin soke matsayin Hong Kong na yanki mai ikon karbar harajin kwstam bisa dokar kansa, da kuma bata matsayin yankin Hong Kong na cibiyar cinikin kasa da kasa, da cibiyar hada-hadar kudi na kasa da kasa, da na cibiyar tashar jiragen ruwa ta kasa da kasa. Kana, dokar ta kuma bata moriyar kamfanonin kasar Amurka dake yankin Hong Kong, lamarin da ya bata ran kowa da kowa, watau babu wanda zai yi nasara
Shehu malami a jami'ar koyon Sinanci ta yankin Hong Kong, wato CUHK, Lau Siu-kai yana cewa, kasar Amurka tana take 'yancin gwamnatin kasar Sin wajen kula da yankin Hong Kong a fili. 'Yan siyasa a kasar Amurka suna goyon bayan masu tada kayar baya na yankin Hong Kong, domin yin amfani da su wajen hana bunkasuwar kasar Sin, lamarin da ya zama babban kalubale ga tsaron kasar Sin. Don haka, ya zama dole ga kasar Sin ta mai da martini kan kasar Amurka, kuma tabbas matakin ba zai yi wa Amurka dadi ba. (Maryam)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China