Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sharhi: Mulkin danniya na kasar Amurka ba zai yi nasara ba
2019-11-30 20:34:30        cri
A kwanakin baya, kasar Amurka ta zartas da dokarta dangane da batun hakkin dan Adam da tsarin dimokuradiya na yankin Hong Kong na kasar Sin. Ta wannan mataki, ta sake nuna manufarta ta mulkin danniya, da fin karfi, lamarin da ya janyo kin amincewa daga gwamnatin kasar Sin da jama'ar kasar, gami da suka da gamayyar kasa da kasa suka yi mata.

Ma iya cewa mulkin danniya da nuna fin karfi su ne manyan halayen musamman na manufar kasar Amurka a fannin hulda da kasashen waje. Kasar Amurka ta dade tana amfani da karfinta wajen keta dokokin kasa da kasa, gami da ka'idojin da ake bi wajen hulda da sauran kasashe. Ta kan yi watsi da kudurin MDD, gami da kaddamar da yaki kan sauran kasashe, lamarin da ya zama babbar barazana ga tsare-tsaren duniyarmu a fannin tsaro. Haka zalika, ta kan tsoma bakinta cikin harkokin cikin gidan sauran kasashe. Har ma ta kafa wasu dokoki yadda ta ga dama, don saka takunkumi ga sauran kasashe, ko kuma wasu kamfanoni. Wadannan matakan da kasar Amurka ta dauka sun nuna cewa, kasar ta riga ta zama wani babban dalilin dake haddasa tashin hankali a duniya, gami da hana kasashen duniya samun zaman lafiya da ci gaban tattalin arziki.

Tun bayan da aka fara ta da zaune-tsaye a yankin Hong Kong na kasar Sin watanni 5 da suka wuce, kasar Amurka tana ta kokarin ruruta wuta a yankin. Da farko ta fara wasu munanan ayyuka a boye, daga bisani ta fara kokarin ta da kura a yankin ba tare da rufa-rufa ba, ta hanyar kokarin karfafa wa masu nuna karfin tuwo gwiwa.

Duk da cewa ana cikin wani yanayi mai muhimmanci na kokarin kwantar da kurar da ta tashi, da maido da tsari da oda a yankin Hong Kong, amma a daidai wannan lokaci ne, kasar Amurka ta zartas da dokar hakkin dan Adam da dimokuradiya na Hong Kong, don neman kara tsoma baki cikin harkokin kasar Sin, da hanzuga tarzoma a yankin Hong Kong. Wannan mataki ya sa an fahimci yunkurin kasar Amurka na yi wa yankin Hong Kong zagon kasa, da lahanta manufar kasar Sin ta " kasa daya, mai tsarin mulki biyu", tare da burin hana kasar Sin samun ci gaba. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China