Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Amurka na bata lokacinta wajen bata yanayin Hong Kong don nuna adawa da Sin, in ji masanan Nijeriya
2019-11-27 11:24:10        cri

Jiya Talata, an wallafa sharhin shugaban cibiyar nazarin harkokin kasar Sin a Nijeriya, Charles Onunaiju a jaridar Blueprint da jaridar the Nation na kasar. Cikin sharhin, ya ce, bisa manufar "kasa daya mai tsarin mulki biyu", salon zaman rayuwar mutanen yankin Hong Kong bai canja ba, matakin majalisar dokokin kasar Amurka na zartar da wani daftarin dokar kare hakkin dan Adam da dimokuradiyya a yankin Hong Kong ya sabawa tushen ka'idar dangantakar dake tsakanin kasa da kasa, kuma ko da Amurka tana goyon bayan masu tada kayar baya na yankin Hong Kong don neman sanya yankin cikin rashin kwanciyar hankali, to ba za ta cimma mugun burinta ba, domin lokacinta kawai take batawa.

Haka kuma, ya ce, majalisar dokokin kasar Amurka ta yi biris da bukatun al'ummominta a yankin Puerto Rico da ma wadanda ke cikin gida, amma ta zartar da wata doka game da batun yankin Hong Kong na kasar Sin, wanda ya zama abun mamaki kwarai da gaske. Kuma burinta shi ne hura wutar rikici a yankin Hong Kong da kuma bata sunan yankin na cibiyar hada-hadar kudi ta kasa da kasa, domin nuna adawa da gwamnatin kasar Sin.

A halin yanzu, masu tada kayar baya suna ta barnata kayayyaki a titunan Hong Kong, amma kasar Amurka ta mai da jagororin masu tada kayar bayan matsayin manyan bakinta, lamarin da ya bata ran kasa da kasa. Tsarin "kasa daya mai tsarin mulki biyu" shi ne babbar gudummawar da kasar Sin ta bayar a duniya, gwamnatin kasar Sin tana mai da hankali sosai kan gudanar da wannan tsari a yankin Hong Kong. Kasar Amurka ba za ta cimma burinta na sanya yankin cikin rashin kwanciyar hankali ba, kana, bayan yankin Hong Kong ya warware babbar matsalar da ya fuskanta, zai cimma bunkasuwar tattalin arziki da samun zaman lafiya kamar yadda sauran yankunan kasar Sin suke samu. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China