2019-11-21 19:00:53 cri |
A jiya Laraba 19 ga watan nan ne jaridar The Australian ta kasar Australia, ta wallafa wani rahoto mai taken "Masu tsattauren ra'ayin Hong Kong suna tayar da hargitsi a kan tituna", inda Hedley Thomas, babban jami'in jaridar ya yi cikakken bayani kan yanayin da yankin ke ciki a yanzu, ta hanyar gabatar da abubuwan da ya gani da idonsa kai tsaye, ko abubuwan da abokansa dake yankin Hong Kong suka gaya masa da bakinsu.
A cikin rahotonsa, dan jaridar Hedley Thomas ya bayyana cewa, yanzu haka masu tsattsauren ra'ayi suna aikata laifuffuka a kan tituna kamar yadda suke so, kuma mazauna yankin sun yi shiru saboda jin tsoronsu, kana wasu kafofin watsa labarai su ma suna gabatar da labarai sabanin hakikanin yanayin da ake ciki. Kaza lika masu tsattsauran ra'ayin sun rika jifan 'yan sanda da boma-boman na mai, da duwatsu, da sandunan karfe, lamarin da ya kai ga rasuwa da jikkatar wasu da dama, don haka ba zai yiwu a kyale hakan tana aukuwa ba.
Ya ce abun mamakin shi ne masu tsattsauran ra'ayin, sun mayar da 'yan sandan Hong Kong, wadanda suke da kwarewa kan aikinsu, suke kuma rike da makamai masu inganci a matsayin "abokan gaba na al'ummun yankin". A bayyane take cewa, an lura masu tsattsauren ra'ayi su ne abokan gaba na mazauna yankin, saboda su ne masu aikata laifuffuka, a maimakon sojojin neman samar da demokuradiya.
Rahoton wanda ya bayyana ainihin yanayin da yankin Hong Kong ke ciki, ya jawo hankali matuka daga shugabannin hukumomin da abun ya shafa.(Jamila)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China