Kasar Sin ta aike da sammaci ga jakadan Amurka
Mataimakin Ministan harkokin wajen kasar Sin Zheng Zeguang, ya aike da sammaci ga jakadan Amurka dake Beijing, Terry Branstad, domin bayyana rashin jin dadin kasar game da matakin Amurka na amincewa da dokar hakkin dan Adam da Demokradiyya kan HK.
Da yake jaddada cewa HK wani bangare ne na kasar Sin, kuma harkokinta harkoki ne na cikin gidan kasar, Zheng Zeguang, ya ce dokar ta yi katsalandan cikin harkokin cikin gidan kasar Sin, inda ya zargi majalisar wakilan Amurka da yin watsi da gaskiya da kuma hada baki da goyon bayan masu tada rikici da kin jinin kasar Sin.
Ya ce kasar Sin ba za ta sauya kudurinta na kare cikakken 'yanci da tsaro da muradunta na ci gaba ba, tare da aiwatar da manufar 'kasa daya mai tsarin mulki 2' da kuma adawa da duk wani yunkuri na tsoma baki cikin harkokin yankin HK daga waje.
Ministan ya ce, kasar Sin na kira ga Amurka da babbar murya, da ta fahimci batun, kuma ta gaggauta gyara kuskurenta, tare da dakatar da zartar da dokar, ta kuma daina tsokaci ko aiwatar da wani abu da zai zama na tsoma baki cikin harkokin HK da sauran harkokin cikin gidan kasar Sin.
A makon da ya gabata ne, majalisar wakilan Amurka ta aike da dokar kare hakkin dan Adam da Demokradiyya ta HK, tare da wata dokar hana fitar da makaman tarwatsa taron jama'a zuwa hukumomin HK, ga fadar White House. Dukkan dokokin biyu sun samu amincewar majalisar dattawan kasar. (Fa'iza Mustapha)
Labarai masu Nasaba