Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wang Yi: Duk wani yunkuri na kawo cikas a yankin Hong Kong ba zai yi nasara ba
2019-11-25 20:31:07        cri
Mamba a majalisar gudanarwar kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya bayyana cewa, duk wani yunkuri na wargaza yankin Hong Kong ko kawo cikas ga makoma da zaman lafiyar yankin, ba zai yi nasara ba.

Wang ya bayyana hakan ne, lokacin da yake amsa tambayar da wata kafar yada labaran Japan ta yi masa yayin da yake ziyara a Tokyo, yana mai cewa, duk yadda al'amura suka sauya a yankin Hong Kong, abu guda shi ne: Hong Kong wani bangare ne na kasar Sin kana yankin musamman da babu wanda zai iya raba shi da kasar Sin. (Ibrahim Yaya)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China