Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sharhi: Dalilin da ya sa wasu 'yan siyasar Amurka suka goyi bayan masu tada tarzoma a HK
2019-11-23 16:52:43        cri
Babban gidan rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG, ya gabatar da wani sharhi mai taken "Dalilin da ya sa wasu 'yan kasar Amurka suka goyi bayan masu tada tarzoma a Hong Kong".

Sharhin da aka gabatar a jiya, ya ce, a yayin da ake dab da kawo karshen tashe-tashen hankali a Hong Kong, wasu 'yan siyasar Amurka sun fitar da wani shirin doka kan hakkin dan Adam da demokuradiyya na Hong Kong na shekara ta 2019, a wani yunkuri na goyon-bayan masu tada tarzoma a yankin, domin za su yi murna da ganin Hong Kong ta lalace baki daya. Idan ba a daidaita rikicin Hong Kong yadda ya kamata ba, harkokin tattalin arziki da kasuwanci na yankin za su samu koma-baya, wanda zai kai ga kwararru a fannin hada-hadar kudi da na sauran wasu bangarori su bar yankin, al'amarin da zai illata kasuwar kudi gami da tattalin arzikin kasar Sin baki daya.

Har wa yau, sharhin ya ce, akwai wasu 'yan siyasar Amurka wadanda suka yi yunkurin tsoma baki cikin zaben 'yan majalisar dokokin Hong Kong, da nufin lalata yankin gami da shiga sharo ba shanu cikin harkokin kasar Sin. Wadannan 'yan siyasar Amurka suna son amfani da tashe-tashen hankalin da suka barke a Hong Kong don illata manufar "kasa daya mai tsarin mulki biyu", da gurgunta aikin dinke kasar Sin baki daya, ta yadda za'a kawo babban tsaiko ga farfadowar al'ummar kasar.

Sharhin ya kara da cewa, kasar Sin ba za ta ja da baya ba sakamakon matsin lambar da ake mata. Harkokin yankin Hong Kong, harkokin cikin gida ne na kasar Sin, kuma kasar ba za ta amince da duk wani "shirin doka" da aka fitar dangane da yankin ba.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China