Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ofishin kula da harkokin HK da Macau ya yi suka ga matakin majalisar dattijan Amurka
2019-11-20 20:56:31        cri

A yau Laraba ne kakakin ofishin kula da harkokin yankunan Hong Kong da Macau, na majalisar gudanarwar kasar Sin, ya yi kakkausar suka ga majalisar dattijai na Amurka, saboda ta fitar da dokar dake shafar hakkin dan Adam da demokuradiya a yankin Hong Kong na kasar Sin.

Kakakin ya bayyana cewa, laifuffukan da masu tattsauren ra'ayi suka aikata, sun riga sun gurgunta doka da oda a yankin Hong Kong, kuma sun kawo babbar illa ga zaman lafiya da wadata a yankin, har ma sun haifar da barazana ga ka'idar kasa daya tsarin mulki biyu ta gwamnatin kasar. Ya ce hakikanin yanayin da ake ciki yanzu ya shaida cewa, kalubalen da ake fuskantar a yankin Hong Kong, bai jibanci hakkin dan Adam da demokuradiya kadai ba, domin kuwa babban laifi ne dake kawo hadari ga mazauna yankin, sai dai wasu 'yan siyasar Amurka, sun kasa kula da yanayi na gaskiya, suna amfani da ma'auni iri biyu wanda bai dace ba.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China