Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ana fatan dakatar da tashe-tashen hankula a Hongkong da wuri, in ji yan kasuwar Sin a Nijeriya
2019-11-25 10:55:15        cri

A ranar 23 ga wata, aka kafa kungiyar bunkasa masana'antu ta 'yan kasuwar Sin dake kasar Nijeriya a birnin Abuja, fadar mulkin kasar. Kamfanin Lee mai jarin yankin Hong Kong wanda ya dade yana aikin kere-kere a Nijeriya ya lashe zaben shugaban kungiyar karo na farko.

A yayin taron karawa juna sani, a madadin shugaban kamfanin Lee na Hong Kong, babban manaja mai kula da harkokin takalma na arewacin Nijeriya Li Guowei ya bayyana cewa, halin da yankin Hong Kong yake ciki ya zama rikici na siyasa da tattalin arziki da wasu yammacin kasashen duniya suka tayar domin nuna adawa da gwamnatin kasar Sin, musamman ma kan manufarta ta bude kofa ga waje, da kuma neman moriyar kansu. Bayan dawo da yankin Hong Kong kasar Sin, cikin shekaru sama da 20 da suka gabata, kwamitin tsakiya na gwamnatin kasar Sin ya cika alkawarinsa game da aiwatar da manufar "kasa daya mai tsarin mulki biyu" a lokacin da yake gudanar da harkokin yankin Hong Kong. Ya kuma baiwa yankin Hong Kong cikakken 'yanci, kuma bai taba tsoma baki cikin harkokin gidan yankin Hong Kong ba.

Li Guowei ya kara da cewa, za a warware matsalolin da yankin Hong Kong yake fuskanta ta hanyar dakatar da tashe-tashen hankula a yankin. Kuma a matsayin 'yan kasar Sin dake kasashen ketare, suna goyon bayan gwamnatin yankin Hong Kong da ta dauki matakai bisa dokokin yankin, da kuma nuna goyon baya ga 'yan sandan yankin don su kiyaye zaman lafiyar zamantakewar al'umma da tsaron jama'ar yankin, ta yadda za a shimfida zaman lafiya a Hong Kong da kuma farfado da tattalin arzikin yankin. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China