Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Hadin kan Sin da Amurka ne kadai hanya mafi kyau da bangarorin biyu za su bi
2019-10-13 20:10:52        cri

CMG ta ba da wani bayani mai taken "Hadin kan Sin da Amurka ce kadai hanya mafi kyau da bangarorin biyu za su bi" a yau Lahadi. Inda ya nuna cewa, an kawo karshen shawarwarin ciniki da tattalin arziki tsakanin manyan jami'ai a sabon zagaye tsakanin kasashen biyu na kwanaki 2 a Washington a ranar 11 ga wata. Bangarorin biyu na samun ci gaba mai armashi a fannoni daban-daban. Bayan samun wannan labari, kasuwar hanayen jari ta kasa da kasa ta samu karuwa sosai, kuma kasuwa na fitar da wani sako mai karfi na cewa: Daidaita dangantakar ciniki da tattalin arzikin Sin da Amurka ba ma kawai zai kawo amfani ga kasashen biyu ba ne, har ma zai samar da kyawawan damammaki ga duk duniya baki daya.

Bayanin ya kara da cewa, takkadamar ciniki dake dabaibaye bangarorin biyu har tsawon shekara daya da wani abu, kasashen biyu sun fahimci cewa, ya kamata su daidaita bambancin ra'ayinsu bisa ka'idar mutunta juna, da kuma hadin kansu bisa tushen yin amfani da juna da cin moriya tare bisa matakai daban daban, abun da ya kasance hanya da ta fi dacewa da bangarorin biyu za su bi. Kana ya fidda wani sabon tunani da sabuwar hanya wajen cimma matsaya daya kan yarjejeniyar ciniki da tattalin arziki tsakaninsu.

Kazalika, bayanin ya nanata cewa, ana iya ganin makoma bisa tarihi. Sin da Amurka ba za su rabu da juna ba, kamata ya yi a yi hadin kai da samun moriya tare a maimakon yin gaba da juna wanda zai kawo hasara matuka. Bisa yarjejeniyar da aka cimma, bangarorin biyu za su ci gaba da shawarwari a nan gaba, don cimma matsaya daya kan yarjejeniyar ciniki da tattalin arziki. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China