Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ya Kamata A Samar Da Kyakkyawan Sharadi Ga Shawarwarin Dake Tsakanin Sin Da Amurka
2019-09-12 14:42:07        cri
A kwanakin baya, Sin ta gabatar da jerin sunayen kayayyakin da aka janye su daga jerin sunayen kayayyakin da Sin ta kara buga harajin kwastam gare su, da kuma kasar Amurka ta sanar da jinkirta lokacin kara buga harajin kwastam ga kayayyakin Sin da darajarsu ta kai dala biliyan 250 da ake shigar da su zuwa kasar Amurka. Game da wannan batu, an yi nuni da cewa, kafin shawarwarin tattalin arziki da cinikayya a tsakanin Sin da Amurka zagaye na 13 da aka shirya gudana a farkon watan Oktoba, bangarorin biyu sun dauki matakai da nuna sahihancinsu ga juna don samar da kyakkyawan sharadi ga cimma sakamako mai kyau a gun shawarwarin, hakan ya dace da fatan kasa da kasa, da ya kamata a nuna yabo ga hakan. Bisa takaddamar ciniki da shawarwarin da aka yi a tsakanin kasashen biyu har na tsawon shekara fiye da daya, an shaida cewa, babu wani bangare da ya cimma nasara, kuma matakan kara buga harajin kwastam ba za su iya warware matsalarsu ba. don haka, ya kamata a nuna daidaici da girmamawa ga juna, da yin shawarwari da hadin gwiwa cikin lumana, ta hakan za a warware matsalolinsu daga tushe. (Mai fassarawa: Zainab, Ma'aikaciyar sashen Hausa na CRI)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China