Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ta sanar da jerin kayayyakin cinikayyar Amurka da ba za a kara karbar haraji kansu ba
2019-09-11 19:48:07        cri

Kasar Sin tana sane da cewa, babu wanda zai yi nasara a yakin cinikayya, karin haraji da ta sanyawa wasu kayayyakin Amurka don mayar da martani kan matakan da kasar ta daukar bisa ayar dokar ciniki mai lamba 301, shi ma zai yi tasiri ga wasu kamfanoni dake nan kasar Sin. Don haka, kasar Sin tana adawa da tsanantar yakin cinikayya. A yayin da take mayar da martani kan matakin danniyar cinikayya da kasar Amurka ta dauka, a sa'i guda kuma za ta yi kokarin rage mummunan tasirin hakan kan wasu kamfanoni dake kasar ta Sin. Matakin da Sin ta dauka na tsara da kuma sanar da jerin kayayyakin cinikayyar Amurka da ba za a kara karbar haraji kansu ba ya nuna cewa, Sin ta yi la'akari sosai kan moriyar kamfanoninta da na Amurka a yayin da take tinkarar yakin cinikayya da Amurka.

Bisa shawarwarin da kasashen Sin da Amurka suka yi, a farkon watan Oktoba za a shirya shawarwarin tattalin arziki da cinikayya tsakanin manyan jami'an kasashen biyu karo na 13 a birnin Washington, inda bangarorin biyu za su yi kokarin cimma matsaya guda, wannan shi ne fatan da bangarori daban daban ke da shi, ciki har da kamfanonin kasashen biyu. Duk wani irin sakamako da za a samu a shawarwarin, kasar Sin za ta ci gaba da gudanar da ayyukanta yadda ya kamata, tare da tsara manufofi don rage tasirin da takaddamar cinikayya ka iya haifar kan kamfanonin ketare dake nan kasar Sin, za kuma ta kai zuciya nesa wajen tinkarar duk kalubalolin da za su kunno kai. (Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China