Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin da Amurka sun yi amfani da hanyar daidaita matsala da ta dace
2019-10-15 20:11:48        cri

An kawo karshen shawarwarin mayan jami'an Sin da Amurka a sabon zagaye a Washington DC kwanan baya, bangarori biyu sun samu ci gaba mai armashi a fannin aikin gona, kiyaye 'yancin mallakar fasaha, musayar darajar kudi, hidimmar hada-hadar kudi, habaka hadin kai ta fuskar ciniki da dai sauransu, ban da wannan kuma, sun tattauna kan ajandar shawarwari nan gaba da amincewa da hada kai don cimma wata yarjejeniya ta karshe.

Bayan shawarwari kan takaddamar da suka shafi shekara daya da wani abu da suka gabata suna yi, Sin da Amurka sun fahimta cewa, mai da hankali kan moriyar masu sayayya da masu samar da kayayyaki, ita ce mafita don ganin an warware batutuwan da ba su da bambancin ra'ayi mai tsanani a tsakaninsu da farko, kana daga bisani, su daidaita sauran matsaloli bisa mataki-mataki har a kai ga cimma matsaya daya.

Babban ci gaban da aka samu a wannan karo shi ne, bangarorin biyu suna kokarin fito da hanyar da ta dace don warware rikicin dake tsakaninsu bisa dabara a siyasance, matakin da ya biya bukatun kasuwar duniya.

Kasashen biyu sun kai ga cimma matsaya daya cewa: Dangantakar ciniki da tattalin arzikin kasashen biyu shi ne babban tushen kwanciyar hankalin duniya, daidaita wannan dangantaka zai amfanawa Sin da Amurka, har ma zai ba da gudunmawa wajen tabbatar da zaman lafiya da wadata a duniya baki daya. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China