Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kamata ya yi a yi watsi da bambancin ra'ayi don yin musanyar ra'ayi da hadin kai tsakanin Sin da Amurka
2019-10-25 10:13:28        cri

Yau Juma'a CMG ya gabatar da wani bayani mai taken "Kamata ya yi a yi watsi da bambancin ra'ayi don yin musanyar ra'ayi da hadin kai tsakanin Sin da Amurka", inda aka nuna cewa, jiya Alhamis mataimakin shugaban kasar Amurka Mike Pence, ya ba da jawabi kan batun kasar Sin dake shafar tattalin arziki, ciniki, aikin soja, hakkin Bil Adama da addini da dai sauransu, daga cikinsu zancen da ya yi game da manufar Sin kan yankin Xinjiang da ma Hong Kong ya sabawa ka'ida mai tushe kan dangantar kasashe biyu wato "Mutunta juna ta fuskar ikon mallakar kasa da cikakken yankin kasa da gujewa tsoma baki cikin harkokin wani", bayani ya ce, bangarorin biyu dai ba su kama hanya iri daya ba a halin yanzu. Duk da haka burin Mike Pence na kara tuntubar juna da hadin kai tsakanin bangarorin biyu na ingiza warware takaddamar dake tsakaninsu.

Bayani kuma ya jaddada cewa, an samu ci gaba mai armashi cikin shawarwarin tattalin arziki da ciniki a sabon zagaye tsakanin bangarorin biyu, matakin da ya aza tubali mai muhimmanci wajen kulla wata yarjejeniya a mataki-mataki. Ya kamata bangarorin biyu su daidaita batutuwa dake jawo hankalin su bisa tushen mutunta juna, da shimfida yanayi mai yakini, da kuma kokarin hadin kansu da sanin bambanci tsakaninsu, da kuma bin hanya iri daya, da daidaita bambancin ra'ayinsu bisa manufar mutunta juna, kana da habaka hadin kai bisa tushe na amfanawa juna da cin moriyar tare don cimma muradunsu baki daya. Matakai da suka zama hanya daya tilo da bangarorin biyu za su bi wajen cimma matsaya daya dake amfanawa kasashen biyu har ma duk duniya baki daya. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China