Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping ya halarci taron ganawar shugabannin kasashen BRICS karo na 11
2019-11-15 12:25:17        cri

Jiya Alhamis, an yi taron ganawar shugabannin kasashen BRICS karo na 11 a birnin Brasilia, fadar mulkin kasar Brazal. Shugaban kasar Brazil Jair Bolsonaro ne ya jagoranci taron, wanda shugaban kasar Sin Xi Jinping, shugaban kasar Rasha Vladimir Putin, firaministan kasar Indiya Narendra Modi, da shugaban kasar Afirka ta Kudu Matamela Cyril Ramaphosa suka halarta. A yayin taron, shugabannin kasashen sun yi musayar ra'ayoyi kan hadin gwiwar dake tsakanin kasashen BRICS da manyan batutuwan dake jan hankulansu, bisa babban taken taron wato "karuwar tattalin arziki za ta ba da gudummawa ga samar da sabbin fasahohi", inda suka kuma cimma matsaya daya kan batutuwan da suka tattauna akai.

Har ila yau cikin wannan taron, Xi Jinping ya gabatar da muhimmin jawabi mai taken "Mu hada kai wajen bude sabuwar shafi ga hadin gwiwarmu". Inda ya jaddada cewa, ya kamata kasashen BRICS su sauke nauyin dake wuyansu yadda ya kamata, da kuma raya harkokin ciniki dake tsakanin kasa da kasa, domin kiyaye yanayin duniya mai zaman karko. Sa'an nan kuma, ya ce ya dace kasashen BRICS su kama damar yin kwaskwarima domin samar da sabbin fasahohi cikin wannan sabon zamani, ta yadda za a zurfafa dangantakar abota a tsakanin kasashen BRICS wajen raya harkokin masana'antu. Bugu da kari, ya ce, ya kamata kasashen BRICS su yi koyi da juna, tare da karfafa mu'amalar al'adu dake tsakanin al'ummomin kasashensu. A karshe dai, ya ce, kasar Sin za ta ci gaba da habaka aikin bude kofa ga waje, da kuma raya shawarar "Ziri daya da hanya daya", domin karfafa dunkulewar Asiya da yankin Pacific, har ma da dukkanin bil Adama.

A wannan rana, shugaba Xi Jinping ya kuma halarci taron shawarwari tsakanin shugabannin kasashen BRICS da kwamitocin masana'antu da kasuwanci da bankin BRICS, wato NDB. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China