Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wang Yi ya halarci taron ministocin harkokin wajen kasashen BRICS
2019-07-27 15:58:08        cri
Mamban majalisar gudanarwa kuma ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya halarci taron ministocin harkokin wajen kasashen BRICS a Brazil, wanda ministan harkokin wajen kasar Ernesto Araújo ya jagoranta. Taron ya kuma samu halartar Ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov, da na Afrika ta Kudu Naledi Pandor da kuma na Indiya Vijay Kumar Singh.

Wang Yi, ya nuna cewa, duniya na fuskantar sauye-sauye da ba a taba ganin irinsa ba a wannan karni, kuma kasuwani da kasashe masu tasowa musamman ma kasashen BRICS sun nuna karfinsu sosai, matakin da ya ingiza aikin samun madogara da yawa a duniya. Ya ce kamata ya yi, kasashen nan biyar sun kara ba da gudunmawarsu wajen gabatar da karin manufofi da bayyana karfin BRICS yadda ya kamata yayin da suke fuskantar sabon yanayi da kalubale.

Mahalarta taron wakilan kasashen biyar, sun yi musayar ra'ayi kan halin da duniya ke ciki da kuma batutuwan shiyya-shiyya da suka fi jan hankalin mutane, inda suka kai ga matsaya daya cewa, ya kamata a kiyaye muradu da ka'idojin kundin mulkin MDD, da kiyaye kasancewar bangarori daban-daban a duniya da yin ciniki cikin 'yanci, kana da kin yarda da ra'ayoyi na kashin kai, da kara karfin daidaita harkokin duniya, da kafa al'umma mai kyakkyawar makoma ga Bil Adama.

Ban da wannan kuma, sun cimma matsaya daya kan magance batutuwan shiyya-shiyya masu jan hankalin kasa da kasa ta hanyar yin shawarwari, da kara hadin kan kasashen BRICS ta yadda jama'arsu za su ci gajiya. Dadin dadawa, kasashen biyar za su yi hattara game da matakin fakewa da batun tsaron Intanet don dakile bunkasar kimiyya da fasahar sauran kasashe, kuma sun yarda da yin kokarin shimfida wani yanayin amfani da kimiyyar sadarwa mai bude kofa kuma da maras nuna bambanci. Wakilan BRICS sun jinjinawa ci gaban da suka samu ta fuskar hadin kansu tare da bayyana niyyarsu ta samun karin ci gaba a taron shugabannin BRICS da za a yi a watan Nuwamban bana. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China