Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An gudanar da taron dandalin mu'amalar al'adu na kasashen BRICS a birnin Brasilia
2019-11-14 12:31:36        cri
A yayin da ake gudanar da taron ganawar shugabannin kasashen BRICS karo na 11 a birnin Brasilia na kasar Brazil, an yi taron dandalin mu'amalar al'adu na kasashen BRICS, wato bikin watsa fim na labarin gaskiya mai taken "Yara da Alfahari" da kasashen BRICS suka kirkire cikin hadin gwiwa.

Babban darekta na wannan fim, da wasu wakilan hukumomin masana na kasashen BRICS kimanin 200 sun halarci wannan taro, inda suka yi tattaunawa mai zurfi bisa taken taron, wato "karfafa mu'amalar al'adu domin inganta hadin gwiwar kasashen BRICS". (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China