Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Peng Liyuan ta halarci aikin uwar gidan shugabnanin kasashen BRICS
2019-11-14 20:19:56        cri

A yammacin ranar 13 ga wata, agogon Brazil, uwar gidan shugaban kasar Sin Xi Jinping madam Peng Liyuan ta halarci biki da aka shiryawa matan shugabannin kasashen BRICS, bisa gayyatar uwar gidan shugaban kasar ta Brazil.

Madam Peng Liyuan da uwar gidan shugaban kasar Afirka ta Kudu sun ziyarci fadar shugaban kasar Brazil Dawn Palace bisa rakiyar uwar gidan shugaban kasar, yayin ziyarar, sun yi hira da daukar hoto, sun kuma kalli nune-nunen kide-kiden matasa da yaran kasar Barzil suka shirya, sun kuma gaida 'yan wasa, inda madam Peng ta bayyana cewa, ziyarar da take yi wannan rana ta burge ta matuka saboda fasahar al'adun kasar ta musamman, duk da cewa, akwai nisa sosai tsakanin kasar Sin da Brazil, amma zumuncin dake tsakaninsu yana kara zurfafa.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China