2019-09-27 10:55:17 cri |
Da yake ganawa a jiya, da ministocin harkokin wajen kasashen BRICS a gefen taron babban zauren MDD karo na 74, Wang Yi ya ce karkashin jagorancin shugabannin kasashen 5, hadin gwiwar BRICS na kara danko, haka ma tasirinta.
Ya ce dangantakar kasashen ta kasance mai daidaita matsalolin kasa da kasa, kana misali na sabon nau'in dangantakar kasa da kasa.
Kasashen 5 sun hada da Brazil da Rasha da Indiya da Sin da Afrika ta Kudu.
Da yake bayani game da damarmaki da kalubalen da kungiyar ta fuskanta, ministan ya yi kira ga kasashen su ci gaba da raya dangantakarsu, da fadada fannonin hadin gwiwa da daukaka dangantakar zuwa mataki na gaba domin kara karfi da girman BRICS. (Fa'iza Mustapha)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China