Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping ya halarci bikin rufe taron dandalin tattanawar masanaantu da kasuwanci na kasashen BRICS
2019-11-14 10:53:12        cri

A jiya Laraba ne aka gudanar da bikin rufe taron dandalin tattaunawar harkokin masana'antu da kasuwanci na kasashen BRICS a birnin Brasilia, fadar mulkin kasa ta Brazil. Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci bikin, inda ya ba da muhimmin jawabi. Kuma, shugabannin kasashen Brazil, Rasha, Indiya da Afirka ta Kudu da sauransu sun halarci bikin.

Cikin jawabin na sa, Xi Jinping ya bayyana cewa, yanayin kasa da kasa ya canja sosai, wanda hakan ya sa ake fuskantar Karin damammaki da kalubaloli. Ya ce "Muna fatan abokanmu a fannonin masana'antu da kasuwanci, za su iya yin amfani da damammaki dake gabansu, yayin da ake tinkarar kalubaloli yadda ya kamata. Haka kuma, da fatan za su dukufa wajen karfafa hadin gwiwar tattalin arziki dake tsakanin kasashen BRICS, su zuba jari a kasashen BRICS cikin himma da kwazo, domin ba da gudummawa ga bunkasuwar tattalin arzikin kasashen, da kuma samar da karin guraben aikin yi.

Bugu da kari, shugaba Xi ya jaddada cewa, bunkasuwar kasar Sin za ta samar da damammakin neman ci gaba ga kasa da kasa. A nan gaba, kasar Sin za ta kara bude kofa ga waje, tattalin arzikin Sin zai kuma ci gaba da karuwa. Haka kuma, Sin za ta kara shigo da hajoji daga kasashen ketare, tare da kyautata yanayin kasuwanci a kasar, domin samar wa kamfanonin dake kasar damammaki masu kyau na neman ci gaba.

Ya kuma kara da cewa, ana gudanar da harkokin shawarar "Ziri daya da hanya daya" kamar yadda ake fata. Ya ce, ana fata kamfanonin kasa da kasa za su yi amfani da wannan dama, su shiga wannan aiki, ta yadda za su sami karin sakamako. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China