Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masanin kasar Afirka ta Kudu: BRICS na taimakawa kasashe masu tasowa wajen fitar da muryarsu
2019-11-13 11:04:49        cri

Shugabannin kasashen BRICS, wato su Brazil, Rasha, India, Sin, da Afirka ta Kudu, za su hadu a Brasilia, hedkwatar kasar Brazil, albarkacin taronsu karo na 11. Dangane da tsarin na BRICS, daraktan cibiyar nazarin harkokin Afirka da kasar Sin a jami'ar Johannesburg ta kasar Afirka ta Kudu David Monyae, ya shaidawa wakilin CRI cewa, tsari kungiyar BRICS ya taimakawa kasashe masu tasowa wajen fitar da muryar su, da kare matsayin tsarin ciniki da ya shafi bangarori daban daban, ta yadda aka samu damar kare moriyar daukacin kasashe masu tasowa.

Haka zalika, David Monyae, ya ce kasar Sin, bisa matsayinta na tattalin arziki mafi karfi tsakanin kasashen BRICS, tana taka muhimmiyar rawa, a kokarin tabbatar da tsarin hadin gwiwa na BRICS. Ya ce kasar Sin tana samar da goyon baya a fannonin kudi, da ilimi, gami da tsare-tsaren raya kimiyya da fasaha.

A ganinsa, jarin da kasar Sin ke zubawa nahiyar Afirka, zai taimaka wa kasashen dake nahiyar raya kansu, gami da cimma burinsu na samun ci gaba mai dorewa, wanda ya shafi dukkan bangarorin al'umma. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China