Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
CMG zai zurfafa hadin gwiwa da lardin Zhejiang
2019-10-08 16:19:12        cri

Yau Talata babban gidan rediyo da talibijin na kasar Sin wato CMG da mahukuntan lardin Zhejiang na kasar sun daddale yarjejeniyar zurfafa hadin gwiwa, inda za su zurfafa hadin gwiwarsu a fannonin gina wani sansanin tsara gajerun shirye-shiryen bidiyo, watsa labaru kan gasar wasannin Asiya ta Hangzhou na shekarar 2022, babban taron Intanet na duniya, shagalin Cartoon da Animation na kasa da kasa na Hangzhou da dai sauransu, a kokarin kafa muhimmin dandamalin watsa labaru ta sabbin hanyoyi, wanda zai bude kofa ga ketare, kuma zai kansance kan gaba a kasar Sin da ma Asiya baki daya.

Shugaban CMG Shen Haixiong, da wasu kusoshin mahukuntan lardin Zhejiang, sun halarci bikin dadddale yarjejeniyar.

A cikin jawabinsa a yayin bikin, Shen Haixiong ya ce, tun bayan kafuwarsa, CMG yana kara azama kan yin hadin gwiwa da sassa daban daban da wurare daban daban na kasar bisa dimbin albarkatunsa da kuma kyakkyawan tambarinsa na kasuwanci. Yadda zai zurfafa hadin gwiwarsa da lardin Zhejiang daga manyan tsare-tsare, wani mataki ne da ya dauka domin kyautata tsare-tsare da kuma kara azama kan ci gabansa yadda ya kamata. CMG yana kokarin taka rawarsa a matsayin babbar kafar yada labaru, da kuma bada taimako wajen raya tattalin arziki da zamantakewar al'ummar wurare daban daban na kasar Sin. Tabbas, hadin gwiwar dake tsakanin CMG da lardin Zhejiang za ta taimaka wajen yin gyare-gyare da raya lardin na Zhejiang. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China