Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban kasar Sin ya isa Brazil domin halartar taron BRICS
2019-11-13 10:26:09        cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya isa kasar Brazil a jiya Talata, domin halartar taron shugabannin kasashen kungiyar BRICS karo na 11.

Taron na BRICS, wanda zai hallara shugabannin kasashe mambobinsa, wato Brazil, da Russia, da India, da Sin da Afirka ta kudu, zai gudana ne a Brasilia, fadar mulkin Brazil, a ranekun Laraba da Alhamis.

Gabanin isa kasar Brazil, shugaba Xi ya gudanar da ziyarar aiki a kasar Girka. (Saminu Hassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China