Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Neman sabuntawa zai habaka hadin gwiwar dake tsakanin kasashen BRICS
2019-11-13 11:21:26        cri

Daga ranar 13 zuwa ranar 14 ga wata, za a yi taron ganawar shugabannin kasashen BRICS a birnin Brasilia, fadar mulkin kasar Brazil. Babban taken taro na wannan karo shi ne "bunkasuwar tattalin arziki zai ba da taimako wajen neman sabuntawa".

Cikin farkon shekaru 10 na hadin gwiwar kasashen BRICS, an cimma sakamako da dama, lamarin da ya sa, a halin yanzu, kasashen BRICS suka zama manyan kasashe masu inganta bunkasuwar tattalin arzikin duniya, da kuma ba da gudummawa ga kyautatuwar tsarin gudanarwar harkokin kasa da kasa.

Haka kuma, kwaskwarimar da ake yi a halin yanzu a fannonin kimiyya da fasaha, da raya masana'antu, ta ba da kyawawan damammaki ga bunkasuwar kasa da kasa. Amma ana fuskantar kalubaloli da dama wajen raya tattalin arziki, domin ra'ayoyin kariyar ciniki, da bin ra'ayin kashin kai da wasu kasashen suke nunawa. Don haka, ya kamata kasashen BRICS su mai da hankali kan bude kofa ga waje domin cimma moriyar juna, da kuma neman sabuntawa domin samun ci gaba cikin nan da shekaru 10 na biyu mai zuwa na hadin gwiwarsu.

Haka kuma, ganawar shugabannin kasashen BRICS, za ta mai da hankali kan neman karuwa da sabuntawa. Ya kamata kasashen BRICS su tsayawa tsayin daka wajen yin hadin gwiwa domin neman moriyar juna, da kafa tsarin tattalin arziki mai bude kofa ga waje, da neman sabunta fasahohi, da kuma neman sabbin hanyoyin raya kasa. A sa'i daya kuma, ya dace su kiyaye tsarin cinikin dake tsakanin bangarori daban daban, da kuma kare babbar ka'ida ta huldar dake tsakanin kasa da kasa, ta yadda za a raya yanayin kasa da kasa bisa ka'idar adalci yadda ya kamata.

Bugu da kari, ya kamata kasashen BRICS su karfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu, domin inganta kwaskwarimar da ake yi kan tsarin gudanarwar harkokin kasa da kasa, da kuma ba da gudummawa kan neman bunkasuwar kasa da kasa, tare da kuma kyautata tsarin kasa da kasa. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China