Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Tashar wasannin CCTV ta dakatar da alaka da Houston Rockets
2019-10-07 15:25:15        cri

Tashar dake watsa wasanni ta CCTV ta babban rukunin gidan rediyo da talabijin na kasar Sin CMG, ta dakatar da duk wata alaka da kungiyar wasan kwallon kwando ta Houston Rockets, har ma da watsa wasannin kungiyar.

CMG yana adawa da wasu kalaman da ba su dace ba, da babban manajan kungiyar Daryl Morey ya furta game da harkokin yankin Hong Kong. Ita ma kungiyar wasan kwallon kwando ta kasar Sin, ta sanar da dakatar da mu'amula da ma hadin gwiwa da kungiyar ta Houston Rockets.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China