Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Za a iya kallon kasaitattun bukukuwan murnar cikar shekaru 70 da kafuwar sabuwar kasar Sin bisa fasahar 4K a gidajen silima 70 a kasar
2019-09-27 19:27:08        cri

Ranar 1 ga watan Oktoba, rana ce ta cika shekaru 70 da kafuwar jamhuriyar jama'ar kasar Sin, inda babban gidan rediyo da talibijin na kasar Sin CMG, zai nuna hoton bidiyo kai tsaye, kan yadda za a gudanar da kasaitattun bukukuwa a ranar, a gidajen silima guda 70 a duk fadin kasar.

Wannan ne karo na farko da za a yi amfani da fasahar 4K cikin gidajen silima. 'Yan kallo daga larduna fiye da 10 na kasar, za su samu damar ganewa idanunsu yadda za a gudanar da babban taron murnar cika shekaru 70 da kafuwar jamhuriyar jama'ar kasar Sin, da babban faretin soja, da jerin gwanon al'umma.

An yi hasashen cewa, 'yan kallon ba za su manta da jin dadin kallon kasaitattun bukukuwan da za a haska ta gidajen silima ba. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China