Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
'Yan sandan Hong Kong sun yi kira da a kiyaye tsaron lafiyar al'umma da dawo da odar zamantakewar al'umma
2019-08-20 13:35:12        cri

Ranar 19 ga wata, bangaren 'yan sandan yankin musamman na Hong Kong na kasar Sin ya shirya taron manema labaru a hedkwatarsa, inda a cewarsa, 'yan sandan za su kara karfin aiwatar da doka, za kuma su bi bahasin aikace-aikacen da suka saba wa doka.

Bangaren 'yan sandan ya nuna cewa, 'yan sandan Hong Kong sun kai zuciya nesa sosai, amma masu zanga-zanga sun rika wuce iyakar doka. Tun daga ranar 9 ga watan Yunin bana har zuwa yanzu, an kama mutane 748 baki daya, inda aka shigar da karar wasu 115 daga cikinsu. An kuma kama mutane 6 da ake tuhuma da nuna karfin tuwo a filin jiragen sama na kasa da kasa na Hong Kong.

'Yan sandan sun kara da cewa, 'yan sandan sun yi hakuri sosai yayin da suke kokarin tabbatar da odar zamantakewar al'umma da tsaron lafiyar mazauna wurin. Ba su yi amfani da karfi ba, sai da wasu suka tada zaune tsaye, ko kuma saba wa doka ta hanyar nuna karfin tuwo, lamarin ya yi barazana ga lafiyar wadanda suke wurin. Har ila yau 'yan sandan su yi kira ga masu zanga-zanga da su nuna sanin ya kamata, lumana da kaucewa nuna karfin tuwo yayin da suke zanga-zanga, a kokarin tabbatar da tsaron lafiyar al'umma da odar zamantakewar al'umma. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China