Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mazauna Hong Kong dubu 476 sun yi gangami domin nuna adawa da karfin tuwo
2019-08-17 20:31:50        cri

Yau Asabar ne Kawancen kiyaye Hong Kong ya shirya wani babban gangami a wurin shan iska na Tamar dake Admiralty a yankin musamman na Hong Kong na kasar Sin.

Masu shirya gangamin sun nuna fatansu na ganin wannan gangami mai taken "yaki da nuna karfin tuwo don kubutar da Hong Kong" ya bayyana ra'ayin al'ummar yankin na kin yarda da nuna karfin tuwo ta kowane salo.

An ruwaito malaman masu shirya gangamin cewa, mutane kimanin dubu 476 sun halarci gangamin a yau. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China