Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An fara watsa shirin " Bayanan magabata da shugaba Xi yake so" a Girka
2019-11-09 20:18:29        cri
A ranar 10 ga wata, za a fara watsa shirin talabijin na "Bayanan magabata da shugaba Xi Jinping yake so" na harshen Girka a shafin intanet na gidan talabijin na Skai na kasar Girka. Babban gidan rediyo da talabijin na kasar Sin CMG ne ya shirya wannan shiri, kuma a kafar watsa labarai mafi tasiri a kasar Girka, wato kamfanin dillancin labarai na Skai za a watsa wannan shiri. Kana, a ranar 10 ga wata kuma, za a fara watsa shirin a shafin intanet na harshen Girka na babban gidan rediyo da talabijin na CMG.

Bugu da kari, za a fara watsa wannan shiri ne kafin ziyarar aiki da shugaba Xi Jinping zai kai ga kasar Girka. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China