Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi ya tattauna da Macron
2019-11-06 15:18:06        cri

A yau ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya tattauna da takwaransa na kasar Faransa Emmanuel Macron a babban dakin taron jama'a dake birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.

Yayin ganawar, shugaba Xi ya bayyana cewa, sun kaiwa juna ziyarar mutunta juna, yayin bikin cika shekaru 55 da kulla huldar diflomasiya tsakanin kasashen, da ma daga matsayin alakarsu zuwa mataki na gaba.

Shugaba Xi ya kuma yi alkawarin hada kai da Macron, don kara bunkasa alakar kasashen biyu bisa manyan tsare-tsare, bisa la'akari da halin da duniya ke ciki, da makoma da batutuwan da suka shafi jama'a, da ba da muhimmanci ga alakar manyan kasashen.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China