Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi da mai dakinsa sun gana da shugaban Faransa da uwar gidansa
2019-11-06 10:22:27        cri

A jiya Talata shugaban kasar Sin Xi Jinping da mai dakinsa Peng Liyuan sun gana da shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron da uwar gidansa Brigitte Macron a birnin Shanghai.

A lokacin isarsu lambun shakatawa na Yuyuan, Macron da mai dakinsa sun samu kyakkyawar tarba daga shugaba Xi da madam Peng. Ma'auranta biyu sun kewaya cikin lambun domin samun nishadi.

Xi ya ce, yana maraba da sake ziyarar da Macron ya kawo kasar Sin da kuma ziyartar Shanghai a karon farko.

Shugaba Xi ya ce, "Ni da mai dakina mun zabi lambun shakatawa na Yuyuan domin karrama shugaban Faransa da mai dakinsa don su more lambun shakatawa na Sinawa da al'adun Sinawa".

A cewar shugaban kasar ta Sin, al'adu daban daban suna cudanya da juna cikin lumana. A matsayin wani bangare na kyautatuwar alakar wakilan gabashi da yammaci, ya kamata kasar Sin da Faransa su mutunta junansu, su yi cudanya da juna, kana su koyi darrusa daga junansu.

A nasa bangaren, Macron ya ce, Faransa tana maraba da manufar kara bude kofar kasar Sin, ya kara da cewa, Faransa a shirye take ta zurfafa hadin gwiwa a harkokin kasa da kasa domin gina tsarin tattalin arzikin kasa da kasa wanda zai amfanawa dukkan bangarori.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China