Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi zai kai ziyara Girka tare da halartar taron kolin BRICS a Brazil
2019-11-07 09:32:03        cri

Mai Magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying, ta bayyana cewa, bisa gayyatar da takwarorinsa na kasashen Girka Prokopis Pavlopoulos da na Brazil Jair Messias Bolsonaro suka yi masa, shugaban kasar Sin Xi Jinping zai kai ziyarar aiki kasar Girka kana zai halarci taron kolin kungiyar BRICS karo na 11 da zai gudana a Brasilia, babban birnin kasar Brazil, daga ranar 10 zuwa 15 ga watan Nuwanba.

Kungiyar kasashen BRICS dai, kungiyar kasashe ne da tattalin arzikinsu ke bunkasa, da suka hada da Brazil, da Rasha, da Indiya da Sin da kuma Afirka ta Kudu.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China