![]() |
|
2019-11-07 20:14:05 cri |
Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin Qin Gang, ya bayyana a yau Alhamis cewa, ziyarar shugaba Xi a kasar Girka, za ta raya dangantakar dake tsakanin Sin da kasashen Turai, tare da karfafa hadin gwiwar dake tsakanin bangarorin biyu game da shawarar "Ziri daya da hanya daya".
Kana, halartar shugaba Xi taron ganawar shugabannin kasashen BRICS, zai kasance muhimmin aikin diflomasiyya da kasar Sin za ta yi, da sauran kasashe masu tasowa, da ma kasashe masu saurin samun bunkasuwar tattalin arziki. (Maryam)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China