Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
CMG ta fara yin gyare-gyare daga dukkan fannoni domin samun nagartaccen ci gaba
2019-09-26 20:09:15        cri

Yau 26 ga wata, rana ce ta cika shekara guda da shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya aike da wasikar murnar cikon shekaru 60 da kafuwar gidan talibijin na kasar Sin na CCTV, da kuma kaddamar da sha'anin watsa shirye-shiryen gidan telibijin. CMG ta fara yin gyare-gyare kan shirye-shiryenta daga dukkan fannoni, domin samun nagartaccen ci gaba.

Babban jami'in CMG ya yi bayani da cewa, gyare-gyaren da aka fara yi, muhimmin mataki ne da aka dauka wajen aiwatar da muhimmin umurnin shugaba Xi Jinping kan ayyukan CMG a tsanake, da gaggauta zurfafa ci gaban hadewar kafofin yada labaru, da kafa babbar kafar yada labaru ta sabon salo a duniya. Kana kuma, za a jarrada kwarewar CMG wajen yayata harkokin murnar cikar shekaru 70 da kafuwar jamhuriyar jama'ar kasar Sin, ta sabbin hanyoyi cikin hadin gwiwar dukkan ma'aikatan CMG.

Jami'in ya kara da cewa, za a yi amfani da wannan dama don kara fadada hanyoyin yayata kasar Sin, a kokarin kafa babbar kafar yada labaru ta sabon salo a duniya, wadda za ta gwanance wajen yayata kasar Sin, tare da ba da jagora, da babban tasiri a duniya. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China